<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>161</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Babban malami ne ya zo da dare
 A wurin Yesu don ya tambaye shi
 Zancen hanyar ceto, har Yesu ya ce,
 &quot;A haife ka kuma.&quot;

[V2]
 KORUS
 Dole a haife ka, a sake haihuwarka,
 Hakika, mai neman shiga Sama can
 Dole haihuwa sau biyu.

[V3]
 2) Ku mutane duk, kasa kunne a nan
 Ga zancen Yesu Ubangijinmu dai,
 A bin da ya ce ya shafe mu duka,
 &quot;A haife ku kuma.&quot;
 Korus

[V4]
 3) Idan kana so ka kai wurin Allah,
 Ka huta a cikin gidan daraja,
 Idan kana son rai na har abada,
 A haife ka kuma.
 Korus

[V5]
 4) &quot;Zancen nan da wuya, ba dama.&quot; ka ce
 Ka zo wurin Yesu, zai yiwu sosai
 Shi yana da ikon al'ajabi fa,
 Zai sake haihuwarka.
 Korus</lyrics>
<title>Babban Malami Ne Ya Zo da Dare LW161</title>
</song>